Lafiri ya kori tsohon dan wasan Arsenal kan kuskuren fahimtar suna

Lokacin da alkalin wasa Dean Hulme ya ba wa Sanchez Watt Hakkin mallakar hoto Others
Image caption Sanchez Watt ya cika da mamaki lokacin da alkalin wasa Dean Hulme ya ba shi jan kati

Saboda kasa bambancewa tsakanin "Watt." "What?" "Watt!" Wani alkalin wasa ya kori tsohon dan wasan Arsenal Sanchez Watt a lokacin da ya tambaye shi sunansa domin ya ba shi katin gargadi, saboda lafirin ya dauka rashin da'a ya yi masa da fadin sunan, inda ya ji kamar ya dawo masa da tambayar.

A lokacin wasan gasar lig ta Ingila ta National League South tsakanin kungiyar dan wasan Hemel Hempstead Town da kungiyar East Thurrock United, alkalin wasa Dean Hulme ya tambayi Sanchez Watt mai shekara 27 sunansa lokacin da ya yi laifi zai rubuta sunansa ya ba shi katin gargadi.

Da dan wasan ya gaya masa sunan, kuma ya sake maimaitawa da ya kara tambayarsa, saboda sunan ya yi kama da kalmar tambaya ta ''What'' ta Ingilishi , sai lafirin ya dauka ya yi masa rashin da'a ne da dawo masa da tambayar har sau biyu, sai ya dauko jan kati ya ba shi.

Sai dai alkalin wasan ya sauya hukuncin, ya soke katin kuma ya dawo da dan wasan tun kafin ya kai ga fita waje, bayan da aka yi masa bayani cewa ai sunan dan wasan ke nan Watt.

A karshen wasan na ranar Talata wanda Hemel Hempstead ta ci 2-0, alkalin wasan ya nemi afuwa, tare da nuna yadda abin ya ba shi dariya shi kansa.

Shi dai Watt ya yi wa Arsenal wasa uku a gasar cin kofin League lokacin yana shekara 18, inda ya ci West Brom a zagaye na uku na gasar a filin wasa na Emirates ranar 22 ga watan Satumba na 2009.