Zakarun Turai: Man City ta kai wasan dab da na kusa da karshe

Michael Lang lokacin da ya ci Manchester City Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Michael Lang ya ci Manchester United da City a bana a gasar ta Zakarun Turai

Manchester City ta yi nasarar zuwa matakin wasan dab da na kusa da karshe na gasar Zakarun Turai duk da kashin da ta sha a gidanta 2-1 a hannun FC Basel saboda ta casa bakin nata 4-0 a karawar farko da suka yi ta matakin na kungiyoyi 16.

Manchester City wadda wannan shi ne karon farko da aka doke ta a gida tun 2016 a gasar ta yi nasara ke nan da jumullar kwallo 5-2 a karawar biyu.

Gabriel Jesus ne ya fara ci wa City wadda kociyanta Pep Guardiola ya ajiye yawancin gwanayen 'yan wasansa, a minti takwas da take leda bayan da Bernardo Silva ya aika bal din ta gefe.

To amma kuma Mohamed Elyounoussi ya farke bal din bayan minti tara kacal, kafin kuma Michael Lang ya kara ta biyu a ragar ta Manchester City.

Manchester City ta yi nasarar wuce zagayen kungiyoyi 16 ne sau daya kawai a karo shida da take zuwa matakin a jere a gasar ta zakarun Turai a karshen nan, inda ta sha kashi a hannun Real Madrid a wasan kusa da karshe na kakar 2015-16.

Za a fitar da jadawalin wasannin dab da na kusa da karshe a ranar 16 ga watan nan na Maris da karfe 12:00 na rana agogon Najeriya da Nijar.

Sannan za a yi wasannin a makon farko da kuma na biyu na watan Afrilu.