Zakarun Turai: Juventus ta yi waje da Tottenham

Paulo Dybala lokacin da ya ci Tottenham ta biyu Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Juventus ta kai wasan karshe na Zakarun Turai a kakar 2016-17, inda Real Madrid ta doke ta da 4-1

An yi waje da Tottenham daga gasar Zakarun Turai bayan da Juventus ta farfado daga ci 1-0, ta zura musu kwallo biyu, sakamako ya kasance ci 4-3 a karawa biyu, wanda hakan ya kai kungiyar ta Italiya wasan dab da na kusa da karshe.

A karawar farko da suka yi a Italiya sun tashi canjaras 2-2, kuma a fafatawar ta biyu a Wembley Son Heung-min ne ya fara daga ragar Juventus ana minti 39 da wasa.

Sai dai bayan an juya kashi na biyu na wasan a minti na 64 sai Gonzalo HiguaĆ­n ya farke, kafin wasa ya sake nisa a kasa da minti uku tsakani sai kuma Paulo Dybala ya kara cin ta biyu.

Tottenham ta kusa ramawa, a minti na 90, wanda da hakan ta tabbata da sai wasan ya kai ga zuwa lokacin fitar da gwani, bayan wata bal da Son ya kwararo ta kuskure ta yi gefe, sannan kuma Harry Kane ya sa mata kai amma ta doki tirken raga.

Wannan shi ne karon farko da aka doke Tottenham a wasa 1, wadda rabonta da zuwa wasan dab da na kusa da karshe a gasar ta Zakarun Turai tun a kakar 2010-11.

Ita kuwa Juventus rabon da a doke ta tun ranar 22 ga watan Nuwamba, wasa 20 ke nan a jere.

Tottenham yanzu ta kasance kungiyar Ingila ta farko da aka yi waje da ita a gasar ta Zakarun Turai a bana, yayin da Manchester City ta bi layin Liverpool wajen nasarar zuwa wasan dab da na kusa da karshe.

Manchester United da Chelsea za su iya sa a samu kungiyoyin Premier hudu a wasan dab da na kusa da karshe na gasar ta Zakarun Turai, idan suka yi wasanninsu na biyu a mako mai zuwa.

United za ta kara da Sevilla ranar Talata bayan da suka tashi ba ci a wasan farko a Spaniya, kafin kuma Chelsea ta fafata a gidan Barcelona ranar Laraba, bayan da suka yi 1-1 a Stamford Bridge.

Za a fitar da jadawalin wasannin dab da na kusa da karshe a ranar 16 ga watan nan na Maris da karfe 12:00 na rana agogon Najeriya da Nijar.

Sannan za a yi wasannin a makon farko da kuma na biyu na watan Afrilu.