Arsenal na fafutukar farfadowa - Koscielny

Arsene Wenger da Laurent Koscielny
Image caption Koscielny ya ce ba Arsene Wenger kadai ya kamata a tuhuma da halin da Arsenal ke ciki ba

Arsenal na fafutukar farfadowa daga mummunan yanayin da take ciki sakamakon doke ta da aka yi sau hudu a jere in ji dan wasan baya na kungiyar Laurent Koscielny.

Dan bayan mai shekara 32 ya ce: ''Muna cikin mawuyacin hali na koma-baya kuma abu ne mai wuya fita daga ciki, muna bukatar yin tunani na nasara, saboda kwakwalwa ce take tsara wa jiki da kafa komai.

Rashin nasarar da ta yi sau biyu a hannun Manchester City da kuma dokewar da 'yar karamar kungiya ta Sweden Ostersunds FK ta yi mata da kuma kashin da ta sha a hannun Brighton su suka jawo wa Arsene Wenger karin matsin lamba.

A ranar Alhamis din nan ne Arsenal din za ta fafata da AC Milan a wasansu na farko na zagayen kungiyoyi 16 na kofin Europa a San Siro.

Gasar ta kofin Turai na Europa ita kadai ce wata dama da take da, ta daukar kofi a bana, kuma zuwa yanzu ita ce kusan hanyar da za ta iya samun gurbin gasar Zakarun Turai ta gaba bayan da ta rasa damar a karon farko a kakar da ta wuce cikin shekara 20.

Za ta samu tikitin zuwa gasar idan ta dauki kofin, kamar yadda Manchester United ta yi a bara.

Bacin ranar da kungiyar ta gamu da shi ya hada da doke ta da Manchester City ta yi a wasan karshe na kofin Carabao, sannan kuma ga cin da Brighton ta yi mata ranar Lahadi, wanda ya sa Arsenal din ta yi nisa tsakaninta da matsayi na hudu a teburin Premier da maki 13.