'Yan wasan Leicester ba su juya min baya ba - Riyad Mahrez

Riyad Mahrez lokacin da ya farke wa Leicester City cin da Bournemouth ta yi mata Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Mahrez ne ya farke wa Leicester cin da Bournemouth ta yi mata ana dab da tashi a karshen makon da ya wuce

Dan wasan gefe na Leicester Riyad Mahrez ya ce abokan wasansa na kungiyar sun ci gaba da ba shi goyon baya da mu'amulla da shi tun lokacin da yunkurin tafiyarsa Manchester City ya ci tura.

Dan wasan mai shekara 27 ya bar zuwa atisaye bayan da maganar tafiyar tasa lokacin kasuwar saye da sayar da 'yan wasa ta watan Janairu ta gagara.

Daga baya ne ya dawo atisaye tare da 'yan wasan kungiyar har ma ya farke musu bal din da Bournemouth ta ci su a wasansu na karshe.

Mahrez ya nuna nadama a kan lamarin, ya ce yanayi ne mai wuya, amma kuma yanzu ya ce yana son ya manta da komai a kan batun.

Dan wasan na tawagar Algeria wanda ya yi wasa hudu na karshen nan na Leicester ya gaya wa tashar Sky Sports cewa ya ji dadi da godiya kan yadda abokan wasansa suka dauki lamarin.

Ya ce ya kaurace wa kungiyar saboda yana bukatar lokaci ya yi tunani, ya ce a ko da yaushe za ka iya yin nadamar wani abu da ka yi, to amma a lokacin yana ganin abin da ya kamata ya yi ke nan.

Kuma ko a lokacin ma ya ce yana magana da tuntubar 'yan wasan da kociyansu da kowa a kungiyar.