Ko da yaushe Tottenham na sakaci a karshe - Chiellini

'Yan wasan Juventus Gianluigi Buffon da Andrea Barzagli (a dama) da Giorgio Chiellini na murnar fitar da Tottenham Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Giorgio Chiellini ya ce tun kafin wasan farko da kuma na biyu sun san za su sha wuya, amma a karshe za su yi nasara

Dan wasan baya na Juventus Giorgio Chiellini ya ce ya kwana da sanin cewa za su doke Tottenham saboda a ko da yaushe kungiyar ta Premier ta kan yi wani sakaci a karshen wasanta.

Kungiyar ta Italiya ta farfado ne daga baya ta yi nasara da ci 2-1 a wasa na biyu da suka yi ranar Laraba na matakin kungiyoyi 16 na Zakarun Turai a Wembley, a karawa biyu ta yi galaba da ci 4-3 jumulla.

Dan wasan na Italiya mai shekara 33 ya ce tarihi ne na Tottenham za ka ga a ko da yaushe tana samun dama da yawa ta cin kwallo, amma kuma a kowane wasa sai ka ga a karshe sun yi sake an ci su.

Ya ce sun san cewa Tottenham tana da gwanayen 'yan wasa kuma kungiya ce mai kyau, amma kuma suna bayar da dama a ci su a kowa ne wasa.

Chiellini ya kara da cewa: Mun yi imani da tarihi, mun ga yadda ta kasance ranar Talata tsakanin Paris Saint-Germain da Real Madrid. Tarihin yana da amfani, da kwarewa yana da muhimmanci sannan kuma mun yi amfani da iyawarmu.''

Duk da an fitar da Tottenham daga gasar ta Zakarun Turai kociyanta Mauricio Pochettino ya ce yana alfahari da kungiyarsa.