Dubbai sun halarci jana'izar Davide Astori

Dubban mutanen da suka halarci jana'izar Davide Astori Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Kusan magoya baya 8,000 ne suka halarci jana'izar a harabar cocin Santa Croce ranar Alhamis da safe

Dubban magoya baya da kuma wakilan kowace kungiyar gasar Serie A ta Italiya ne suka taru a birnin Florence domin halattar jana'izar kyaftin din Fiorentina Davide Astori.

Dan wasan na baya na tawagar Italiya ya mutu ne ranar Lahadi yana da shekara 31 bayan rashin lafiya na lokaci daya.

'Yan wasan Juventus da suka doke Tottenham a jiya Laraba sun halarci jana'izar, ciki har da kyaftin din kungiyar kuma na Italiya mai tsaron raga Gianluigi Buffon.

Dan bayan Juventus Giorgio Chiellini, wanda ya rika hawaye lokacin da aka yi shiru na minti daya kafin fara wasansu da Tottenham a Wembley, domin tunawa da Astori shi ma ya je tare da kociyansu Massimiliano Allegri.

Za a binne gawar ta Astori ne a birnin Bergamo, inda ya girma kuma har yanzu iyayensa suke zaune a can.