Kofin Europa: Arsenal ta doke AC Milan 2-0

Henrikh Mkhitaryan lokacin da ya ci wa Arsenal AC Milan Hakkin mallakar hoto Others
Image caption Henrikh Mkhitaryan ya ci kwallonsa bakwai daga cikin 12 na karshen nan a gasar Europa

Arsenal ta kawar da matsalolin da take fama da su a kwanakin nan gefe daya ta yi abin a-zo-a-gani wajen doke masu masaukinta AC Milan 2-0, wasan farko na matakin kungiyoyi 16, na kofin Europa.

Gunners din sun je wasan ne a yanayi na koma baya da ba su taba shiga ba a tsawon shekara 22 na jagorancin kociyansu Arsene Wenger, da kuma rashin nasara sau hudu a jere da ake doke su.

Bal din farko ta Henrikh Mkhitaryan a kungiyar ita ce ta sa su gaba a minti na 15 da shiga fili, sai kuma ta biyu wadda Aaron Ramsey ya ci dab da tafiya hutun rabin lokaci.

Da kwallo biyun da Arsenal ta ci yanzu a gidan AC Milan ana ganin tana kusa da samun damar zuwa wasan dab da na kusa da karshe na gasar ta Europa, idan har ta kara yin galaba a karawarsu ta biyu ranar Alhamis mai zuwa a filin Emirates.

Ga sakamakon wasu daga cikin wasannin na Europa na Alhamis:

Atl├ętico Madrid3 - 0 Lokomotiv Moskva

CSKA Moskva0 - 1 Olympique Lyonnais

Borussia Dortmund 1 - 2 Salzburg