Me zai hana Messi buga wasan Barca da Malaga?

Barcelona forward Lionel Messi Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Lionel Messi

Lionel Messi ya janye daga buga fafatawar da Barcelona za ta yi da Malaga ranar Asabar saboda dalilai na "kashin kansa".

Barca ta sanar a shafinta na sada zumunta cewa dan wasan ba zai shiga a karawar ba tana mai cewa ta maye gurbinsa da Yerry Mina.

Ana sa ran mai dakinsa Messi za ta haifi dansu na uku kowanne lokaci daga yanzu.

Barca ce ke kan gaba a saman teburin La Liga kuma za ta fafata da Chelsea a karawa ta biyu a wasan 'yan 16 na gasar cin Kofin Zakarun Turai ranar Laraba.

Labarai masu alaka