Manchester United ta doke Liverpool

Marcus Rashford Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Marcus Rashford ne ya ci wa Manchester United dukkan kwallo biyun.

Marcus Rashford ne ya zura kwallaye biyun da Manchester United ta doke Liverpool sannan ta karfafa matsayinta na kasancewa ta biyu a saman tebirin gasar Premier ta Ingila.

Wannan nasarar na nufin kungiyar, wacce Jose Mourinho ke jagoranta, na ci gaba da cike gibin da ke tsakaninta da Manchester City wadda ke ta daya a tebirin da tsiran maki 13 - akalla dai har sai lokacin wasan da City za ta yi da Stoke ranar Litinin - kuma tana da tazarar maki biyar da Liverpool wacce ke matsayi na uku.

Rashford, wanda ya buga wasansa na farko tun bayan wanda ya buga ranar 26 ga watan Disamba, zai zama dan wasan da manema labarai za su fi tattaunawa a kansa, ko da yake ya ci dukkan kwallayen ne da taimakon Romelu Lukaku.

Kwallon da dan kasar ta Belgium ya doka da ka ce ta isa wurin Rashford wanda nan da nan ya zura ta.

Kwallo ta biyu da Unite ta ci kuwa, Lukaku ne ya rike kwallon sannan ya mika ta ga Juan Mata and, wanda bai samu damar buga ta ba ta fada hannun Rashford wanda ya sake zura ta.

Dawowar da Sanchez ya yi Manchester United daga Arsenal a watan Janairu ta yi tasiri sosai kan 'yan wasan United, ciki har da Rashford, wanda bai buga wasan da ya wuce na minti 100 ba kuma ana sanya shi ne domin maye gurbin wani dan wasan a 2018 kafin wasan na ranar Asabar.

Sai da Rashford ya yi ta jira domin damarsa ta zo, kuma bai yi watsi da ita ba da ta zo din a lokacin da kocin Ingila Gareth Southgate ke kallon wasansu.

Manchester United za ta bi sahun Liverpool da makwabciyarta Manchester City domin buga wasan 'yan-takwas na gasar cin Kofin Zakarun Turai zagaye na biyu, inda za su fafata da Sevilla ranar Laraba, bayan yin 0-0 a Spain.

Labarai masu alaka