Arsenal ta ci kwallo sama da 1,000 a gasar Premier a gida

Arsenal Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Arsenal tana ta shida a kan teburi da makinta 48

Arsenal ta doke Watford da ci 3-0 a wasan mako na 30 a gasar cin kofin Premier da suka kara a ranar Lahadi a Emirates.

Arsenal ta ci kwallo ne ta hannun Shkodran Mustafi kuma na 1,000 da kungiyar ta zura a raga a Premier a gida, bayan da aka dawo daga hutu Pierre-Emerick Aubameyang ya ci na biyu.

Saura minti 14 a tashi daga fafatawar Arsenal ta kara na uku ta hannun Henrikh Mkhitaryan.

Watford ta barar da fenariti, bayan da Petr Cech ya buge kwallon da Troy Deeney ya buga.

A karawar farko da kungiyoyin biyu suka yi a gasar a ranar 14 ga watan Oktoban 2017, Watford ce ta yi nasarar cin Arsenal 2-1.

Da wannan sakamakon Arsenal ta ci gaba da zama ta shida a kan teburin Premier da maki 48.

Watford za ta karbi bakuncin Bournemouth a ranar 31 ga watan Maris, yayin da Arsenal da Stoke City za su kece-raini a ranar 1 ga watan Afirilun 2018.

Labarai masu alaka