Tottenham ta koma ta uku a teburin Premier

Tottenham Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Tottenham tana ta uku a kan teburin Premier da maki 61, ita kuwa Liverpool tana ta biyu da maki 60

Tottenham ta yi nasarar cin Bournemouth 4-1 a wasan mako na 30 a gasar cin kofin Premier da suka fafata a ranar Lahadi.

Bournemouth ce ta fara cin kwallo ta hannun Junior Stanisla daga baya Tottenham ta farke ta hannun Dele Alli kuma haka aka tafi hutun rabin lokaci.

Bayan da aka dawo ne Son Heung-min ya ci wa Tottenham kwallo biyu, sannan Serge Aurier ya kara kwallo a ragar Bournemouth kuma na hudu a wasan.

Da wannan sakamakon Tottenham ta koma ta uku a kan teburin Premier da maki 61, yayin da Liverpool wadda Manchester United ta doke ta 2-1 a ranar Asabar ta koma ta hudu da maki 60.

Kungiyoyi hudu ne za su kai gasar cin kofin Zakarun Turai ta badi kai tsaye daga Ingila.

Labarai masu alaka