Pogba bai halarci atisayen United ba

Man United Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Pogba bai buga wasan da United ta ci Liverpool 2-1 a ranar Asabar ba

Paul Pogba bai halarci atisayen da Manchester United ta yi a ranar Litinin a shirin da take yi domin fuskantar Sevilla a gasar cin kofin Zakarun Turai ba.

United za ta karbi bakuncin Sevilla a wasa na biyu a ranar Talata a Old Trafford, bayan da suka tashi babu ci a karawar farko da suka yi a Spaniya a ranar 21 ga watan Fabrairu.

Pogba mai shekara 24, bai buga wasan da United ta ci Liverpool 2-1 a gasar Cin Kofin Premier da suka yi a ranar Asabar ba.

Bayan Pogba da bai halarci atisayen United ba, haka ma Marcos Rojo da Phil Jones da Ander Herrera da kuma Daley Blind ba su je ba.

Tuni dai Anthony Martial da kuma Zlatan Ibrahimovic suke yin atisaye tare da 'yan wasan Manchester United.

Labarai masu alaka