Man City ta bayar da tazarar maki 16

Manchester City Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Man City ta hada maki 81 a wasa 30 da ta yi a gasar Premier shekarar nan

Manchester City ta yi nasarar cin Stoke City 2-0 a wasan mako na 30 a gasar cin kofin Premier da suka kara a ranar Litinin.

City ta ci kwallayen ne ta hannun David Silva, wanda ya ci na farko a minti na 10 da fara wasa, sannan ya kara na biyu bayan da aka dawo daga hutun rabin lokaci.

Da wannan sakamakon City ta ci gaba da zama a matakinta na daya a kan teburin Premier, ta kuma bai wa Manchester United mai mataki na biyu tazarar maki 16.

Jumulla City ta ci wasan Premier 26, ta yi canjaras a karawa uku aka doke ta wasa daya kacal, ta ci kwallo 85 aka zura mata 20 a raga.

Labarai masu alaka