Al Ahly ta ci kofin gasar Masar karo na 40

Al Ahly Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Al Ahly za ta kara da Mounana a gasar cin kofin zakarun Turai

Kungiyar kwallon kafa ta Al Ahly ta lashe kofin gasar kwallon kafar Masar karo na 40 jumulla.

Al Ahly ta samu wannan damar a ranar Litinin, bayan da Al Masry da Entag El Harby suka tashi wasa babu ci.

Kungiyar wadda Hossam El Badry ke horar da ita, ta yi nasarar cin Enppi a ranar Lahadi.

El Badry ya ce kungiyar za ta mai da hankali wajen lashe kofin kalubalen Masar da na Zakarun Afirka.

Kungiyar Wydad ta Morocco ce ta doke Al Ahly a gasar cin kofin zakarun Afirka a wasan karshe a Casablanca.

Al Ahly za ta ziyarci Gabon a makonnan domin karawa da Mounana a wasan zagaye na kungiyoyi 32 da suke cikin gasar shekarar nan.

Labarai masu alaka