Sevilla ta fitar da United daga gasar Turai

Sevilla Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Sevilla ta kai wasan daf da na kusa da na karshe

An yi waje da Manchester United daga Gasar Cin Kofin Zakarun Turai, bayan da Sevilla ta doke ta 2-1 a Old Trafford.

Sevilla ce ta fara cin kwallo biyu bayan da aka dawo daga hutu ta hannun Wissam Ben Yedder daga baya ne Romelu Lukaku ya farke kwallo daya.

A wasan farko da kungiyoyin biyu suka buga a Spaniya sun tashi karawar babu ci a ranar 21 ga watan Fabrairu.

Da wannan sakamakon, an fitar da United daga gasar bana tare da Tottenham, yayin da Manchester City da Liverpool suka kai zagayen gaba.

Chelsea wadda ta buga kunnen doki 1-1 da Barcelona a Stamford Bridge a ranar 20 ga watan Fabrairu, za ta ziyarci Camp Nou a wasa na biyu a ranar Laraba.

Ita ma Roma ta kai zagayen gaba bayan da ta ci Shakhtar 1-0 a Italiya, a wasan farko Shakhtar ce ta ci Roma 2-1.

Labarai masu alaka