Mark Hughes ne ya dace da Southampton - Robbie Savage

Mark Hughes Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Mark Hughes ya jagoranci Stoke sau uku a jere ta gama gasar Premier a matsayi na tara

Robbie Savage ya ce kamata ya yi Southampton ta dauki Mark Hughes a matsayin sabon kociyanta har zuwa karshen kakar nan.

A ranar Litinin kungiyar ta kori kociyanta Mauricio Pellegrino bayan ta ci wasa daya daga cikin 17, abin da ya sa ta zama maki daya kawai a saman matakin faduwa daga gasar Premier.

A wata hira da ya yi da BBC tsohon dan wasan wanda ke sharhi kan kwallon kafa a yanzu ya ce, za a iya dauka shi mahaukaci ne.

Amma idan aka duba cewa saura wasa takwas a gama gasar ta Premier, kuma idan aka duba kociyoyin da ba su da aiki Mark Hughes ne ya fi dacewa.

Savage wanda ya yi wasa a tawagar Wales da kuma kungiyar Blackburn karkashin Hughes yana ganin kociyan shi ne ya fi cancanta da aikin duk da cewa Stoke City ta kore shi a watan Janairu.

Hughes ya jagoranci kusan wasa 450 na Premier a kungiyoyin Blackburn da Manchester City da Fulham da QPR da kuma Stoke.

Haka kuma ya taka wa Southampton leda na dan wani takaitaccen lokaci a karshen wasansa na kwallon kafa.

Savage ya ce kociyan ya yi wa Southampton, wasa a baya kuma zai so ya nuna wa Stoke cewa sun yi kuskure, saboda yana da kwarewa sosai.

Southampton na fatan nada sabon kociyanta kafin karawar da za ta yi da Wigan ranar Lahadi na neman zuwa wasan dab da na karshe na cin kofin FA.

Duk wanda aka nada zai kasance kociya na biyar na kungiyar tun lokacin da Mauricio Pochettino ya maye gurbin Nigel Adkins.