Chelsea ta ziyarci Barcelona a gasar Turai

Chelsea Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Chelsea da Barcelona sun tashi kunnen doki a Stamford Bridge

Kungiyar Barcelona na karbar bakuncin Chelsea a wasa na biyu da za su kara a Gasar Cin Kofin Zakarun Turai a ranar Laraba a Camp Nou.

Kungiyoyin biyu sun tashi wasa babu ci a fafatawar farko da suka yi a ranar 20 ga watan Fabrairu a Stamford Bridge.

Chelsea da Barcelona sun kara a wasa 16 a tsakaninsu, inda kowacce ta yi nasara a karawa biyar-biyar, sannan suka yi canjaras a wasa shida.

Barcelona ta Lashe Kofin Zakarun Turai karo biyar, ita kuwa Chelsea sau daya ta dauke shi.

Ga haduwa tsakanin Barcelona da Chelsea:

2017/2018 Gasar Cin Kofin Zakarun Turai

 • Chelsea 1 - 1 Barcelona

2011/2012 Gasar Cin Kofin Zakarun Turai

 • Barcelona 2 - 2 Chelsea
 • Chelsea 1 - 0 Barcelona

2008/2009 Gasar Cin Kofin Zakarun Turai

 • Chelsea 1 - 1 Barcelona
 • Barcelona 0 - 0 Chelsea

2006/2007 Gasar Cin Kofin Zakarun Turai

 • Barcelona 2 - 2 Chelsea
 • Chelsea 1 - 0 Barcelona

2005/2006 Gasar Cin Kofin Zakarun Turai

 • Barcelona 1 - 1 Chelsea
 • Chelsea 1 - 2 Barcelona

2004/2005 Gasar Cin Kofin Zakarun Turai

 • Chelsea 4 - 2 Barcelona
 • Barcelona 2 - 1 Chelsea

1999/2000 Gasar Cin Kofin Zakarun Turai

 • Barcelona 5 - 1 Chelsea
 • Chelsea 3 - 1 Barcelona

1965/1966 Gasar Fairs Cup

 • Barcelona 5 - 0 Chelsea
 • Chelsea 2 - 0 Barcelona
 • Barcelona 2 - 0 Chelsea

Labarai masu alaka