Chelsea ta yi ban kwana da Gasar Zakarun Turai

Chelsea Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption A wasan farko da kungiyoyin biyu suka buga a Stamford Bridge a ranar 20 ga watan Fabrairu, sun tashi 1-1 ne

Kungiyar Barcelona ta fitar da Chelsea daga Gasar Cin Kofin Zakarun Turai ta bana, bayan da ta doke ta da ci 3-0 a karawar da suka yi a Camp Nou a ranar Laraba.

Chelsea ta fara cin kwallo ta hannun Lionel Messi, sannan Ousmane Dembele ya kara na biyu.

Bayan da aka dawo daga hutu ne Messi ya kara na uku kuma na biyu da ya ci a fafatawar.

Da wannan sakamakon Barcelona ta kai wasan daf da na kusa da na karshe da kwallo 4-1, bayan da wasan farko a Stamford Bridge suka tashi kunnen doki 1-1.

Ita ma Bayern Munich ta kai zagayen gaba a gasar, bayan da ta ci Besiktas 3-1, jumulla 8-1 gida da waje.

Labarai masu alaka