Arsenal za ta karbi bakuncin Milan a Emirates

Arsenal Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption A ranar Juma'a za a raba jadawalin daf da na kusa da na karshe a Gasar ta Europa

Kungiyar AC Milan za ta ziyarci Emitares domin buga wasa na biyu da Arsenal a gasar Cin Kofin Zakarun Turai ta Europa a ranar Alhamis.

Arsenal ce ta ci Milan 2-0 a wasan farko da kungiyoyin suka buga a ranar a cikin watan Fabrairu a Italiya.

Kuma Aaron Ramsey da Henrikh Mkhitaryan ne suka ci wa Arsenal kwallayen.

Arsenal ta samu kwarin gwiwa bayan da dan wasanta Shkodran Mustafi wanda ya yi rauni a wasan da ta ci Watford a Premier ya murmure.

Haka kuma Hector Bellerin da kuma Nacho Monreal sun samu sauki, yayin da Alexandre Lacazetteda da kuma Santi Cazorla ke yin jinya.

Bayan da Pierre-Emerick Aubameyang ba zai buga wa Arsenal fafatawar ba, ana sa ran Danny Welbeck ne a matakin mai cin kwallo.

Labarai masu alaka