Hukumar kwallon Ingila ta ci tarar Guardiola

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Hukumar ta gargadi Guardiola bayan da ya tashi wasan da Wigan ta ci City a kofin FA

Hukumar kwallon kafar Ingila ta ci tarar kocin Manchester City, Pep Guardiola kan saka zirin kyalle mai ruwan dorawa, bayan da bai ji gargadinsa da hukumar ta yi masa ba.

A lokacin da ta bayyana dalilin cin sa tarar fam 20,000, hukumar ta ce ta rubuta wa Guardiola wasika da dama kan ya guji saka zirin kyallen a rigarsa.

A makon jina ne kocin ya amince da tuhumar da hukumar ta yi masa kan saka alama a rigarsa ta goyon bayan siyasa.

A watan Nuwamba, Guardiola ya ce ya saka zirin ne domin marawa 'yan siyasa da aka daure 'yan kabilarsa ta Catalonia baya.

Hukumar ta tattauna da kocin City kan batun a watan Disamba, bayan da ta gargade shi karo biyu.

Labarai masu alaka