Arsenal ta fara jin kanshin kofin Europa

Europa Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Arsenal tana ta shida a kan teburin Premier da maki 48

Kungiyar kwallon kafa ta Arsenal ta kai zagayen daf da na kusa da na karshe a Gasar Cin Kofin Zakarun Turai ta Europa.

Arsenal ta taka wannan matakin ne bayan da ta ci AC Milan 3-1 a karawar da suka yi a ranar Alhamis a Emirates.

Milan ce ta fara cin kwallo ta hannun Hakan Calhanoglu kuma tazarar minti hudu tsakani Arsenal ta farke ta hannun Danny Welbeck a bugun fenariti.

Bayan da aka dawo ne daga hutu Gunners ta kara na biyu ta hannun Granit Xhaka, sanan Danny Welbeck ya kara na uku kuma na biyu da ya ci a wasan.

Arsenal cin Milan ta yi 2-0 a wasan farko da suka buga a Italiya, hakan ne ya sa ta kai zagayen gaba da kwallo 5-1 gida da waje.

Sauran kungiyoyin da suka kai zagayen gaba a gasar Europa sun hada da Athletico Madrid da Marseile da Lazio da Sporting da Rb Leipzig da RB Salzburg da kuma CSKA Moscow.

Za a raba jadawalin wasannin daf da na kusa da na karshe a ranar Juma'a a Switzerland.

Labarai masu alaka