Mohamed Salah 'na iya maye gurbin Messi '- Jurgen Klopp

Mo Salah and Lionel Messi Hakkin mallakar hoto Reuters/Getty Images
Image caption An fara kamanta bajintar Mohamed Salah da ta Lionel Messi

Kocin Liverpool Jurgen Klopp ya ce Mohammed Salah na kan hanyar zama shahararren dan wasa kamar Lionel Messi bayan da ya zura wa Watford kwallo 4 a jiya Asabar.

Salah ne dan wasan da ke kan gaba a yawan kwallaye a dukkan manyan lig-lig guda biyar na Turai - inda ya tsere wa Lionel Messi na Barcelona da Harry Kane na Tottenham.

Amma klopp ya ce Salah mai shekara 25 da haihuwa ba ya damuwa da abin da wasu 'yan wasan ke yi:

"Ba na jin Mo na son a rika kwatanta shi da Lionel Messi".

"Messi ya shafe tsawon lokaci yana gogewa a wasan kwallo. Kai kace ya shafe shekara 20 yana taka leda."

"Ina ganin dan wasan da ke da irin wannan tasirin a kan wata kungiya sai Diego Maradona."

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Mohammed "Mo" Salah

Shi ma tsohon kyaftin din Liverpool Steven Gerrard ya yi imanin cewa "muna shaida farkon faruwar wani shaharraren dan wasa".

Kwarewar Salah da kamanninsa da Maradona sun sa har ana kamanta shi da yadda Messi ke cin kwallyensa.

'Yan wasan Turai da suka fi cin kwallaye (Daga: Opta)
Sunan dan wasa Yawan kwallo
Mohamed Salah 36
Harry Kane 35
Lionel Messi 34
Ciro Immobile 34
Edinson Cavani 33
Cristiano Ronaldo 33
Robert Lewandowski 32
Sergio Aguero 30
Neymar 28

Salah - tarihin da ya kafa

  • Salah ya zura kwallo 36 a kungiyar Liverpool a dukkan wasannin da ya buga mata - a shekarasa ta farko a kungiyar.
  • Ya ci kwallo 28 a gasar firimiya ta bana - Didier Drogba ne kawai dan wasa daga Afika da ya fi shi kokari (Drogba ya ci kwallo 29 a kakar 2009-2010).
  • Salah shi ne dan Masar na farko da ya fara cin kwallaye uku aa wasa guda a gasar firimiyar Ingila.
  • Salah ya ci kwallo hudu daga shot hudu da ya buga - wannan ne karon farko da wani dan wasan firimiya ya yi haka tun 2009 da Andrey Arshavin ma ya kafa tarihi, shi ma a Anfield.
Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Salah shi ne dan Masar na farko da ya fara cin kwallaye uku aa wasa guda a gasar firimiyar Ingila

Labarai masu alaka