'Yan Real 18 da za su kara da Girona

Real Madrid Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Madrid tana ta hudu a kan teburin La Liga, bayan da aka buga karawa 28

Real Madrid za ta karbi bakuncin Girona a wasan mako na 29 a Gasar Cin Kofin La Liga da za su kece-raini a Santiago Bernabeu a ranar Lahadi.

Tuni kocin Real, Zinedine Zidane ya bayyana 'yan wasa 18 da su fafata da Gironar.

Wannan shi ne karo na biyu da kungoyin biyu za su kara a Gasar ta La Liga, bayan da Girona ta doke Real 2-1 a wasan farko da suka yi a ranar 29 ga watan Oktoban 2017.

Real tana mataki na hudu a kan teburi da maki 57, ita kuwa Girona tana da maki 43 a matsayi na bakwai a wasannin bana.

'Yan wasan Real 18 da za su fuskanci Girona:

Masu tsaron raga: Navas da kuma Casilla.

Masu tsaron baya: Carvajal da Vallejo da Varane da Nacho da Marcelo da kuma Theo.

Masu wasan tsakiya: Kroos da Modric da Casemiro da Asensio da Isco da kuma Kovacic.

Masu cin kwallo: Cristiano Ronaldo da Benzema da Bale da kuma Lucas Vazquez.

Labarai masu alaka