Chelsea ta kai daf da karshe a FA

Chelsea Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Chelsea tana ta biyar a kan teburin Premier da maki 56 da kwantan wasa daya

Kungiyar Chelsea ta kai wasan daf da karshe a Gasar Cin Kofin Kalubalen Ingila na bana, bayan da ta ci Leicester City 2-1 a ranar Lahadi.

Morata ne ya fara ci wa baki kwallo saura minti uku a tafi hutun rabin lokaci, bayan da aka dawo ne Jamie Vardy ya farke, inda karawar ta kai ga karin lokaci.

Pedro ne ya ci wa Chelsea kwallo na biyu a minti na 105, hakan ne ya kai Chelsea wasan daf da karshe a gasar shekarar nan.

Kungiyoyin da suka kai wannan matakin sun hada da Manchester United wadda ta ci Brighton 2-0 a ranar Asabar, ita kuwa Tottenham ta doke Swansea 3-0.

A ranar Lahadi ne sabon kofin Soutahmpton, Mark Hughes ya kai kungiyar wasan daf da karshe a kofin FA, bayan da ya yi nasarar cin Wigan 2-0.

Labarai masu alaka