United za ta kara da Tottenham ranar Asabar

Premier Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption United tana ta biyu a kan teburin Premier, yayin da Tottenham ke ta hudu

Hukumar kwallon kafa ta Ingila ta tsayar da ranar da za a buga wasan daf da karshe a Gasar Cin Kofin FA, tsakanin Manchester United da Tottenham.

United wadda Jose Mourinho ke jan ragama, za ta karbi bakuncin Tottenham a ranar 21 ga watan Afirilu a Wembley filin da Spurs ke murza-leda a bana.

Kungiyoyin biyu sun kara a Gasar Premier ta shekarar nan, Inda United ta ci Tottenham 1-0 a ranar 28 ga watan Oktoba, ita kuwa Tottenham 2-0 ta doke United a ranar 31 ga watan Janairun 2018.

Daya wasan daf da karshen za a yi shi ne tsakanin Chelsea da Southampton a ranar 22 ga watan Afirilu a Wembley.

Chelsea ta ci Southampton 1-0 a wasan Premier da suka kara a Stamford Bridge a ranar 16 ga watan Disambar 2017.

Haka kuma hukumar ta ce za ta yi amfani da na'urar da ke taimakawa alkalin wasa tantance shigar tamaula raga.

-------------------------------------------------------------------------------------------------------------------------------------------------------------------------------

Hukumar kwallon kafa ta Ingila ta raba jadawalin Gasar Cin Kofin Kalubalen kasar a wasannin daf da karshe a ranar Lahadi.

Jadawalin ya nuna cewar Manchester United za ta kara da Tottenham, yayin da Chelsea za ta kece-raini da Southampton.

Wasannin na Cin Kofin Kalubalen ya koma tsakanin kungiyoyin da ke buga Premier, inda Manchester United ta kai wannan matakin bayan da ta ci Brighton 2-0 a ranar Asabar.

Tottenham kuwa Swansea ta ci 3-0 a ranar ta Asabar, ita kuwa Chelsea ta doke Leicester City 2-1, yayin da Southampton ta ci Wigan 2-0 a ranar Lahadi.

Za a yi wasannin ne a Wembley tsakanin 21 zuwa 22 ga watan Afirilun, 2018.

United wadda ke matsayi na biyu da kwantan wasa daya a teburin Premier tana da kofin FA 12, ita kuwa Tottenham mai kwantan wasan Premier ta hudu a kan teburi tana da FA takwas.

Chelsea ita ma mai kwantan wasa daya a Premier kuma ta biyar a teburi ta lashe kofin sau bakwai, inda Southampton ta 18 ta taba ci sau daya a 1976.

Labarai masu alaka