Yaushe Messi zai kamo Ronaldo a cin kwallo?

Messi da Ronaldo Hakkin mallakar hoto DOMINIQUE FAGET
Image caption Ronaldo da Messi sun mamaye fagen kwallon kafa na tsawon shekaru inda ba a jin duriyar kowa sai su

Real Madrid ta ci Girona 6-3 a gasar La Liga wasan mako na 29 da suka kara a ranar Lahadi a Santiago Bernabeu.

Wannan ne shi ne karo na 50 da Cristiano Ronaldo ya ci kwallo uku a wasa daya a tarihin kwallonsa.

Abin da ya sa wasu ke cewa yaushe abokin hamayyarsa Lionel Messi zai kamo shi - sau 44 Messi ya ci kwallo uku a wasa guda.

Har ila yau Ronaldo na gaban Messi wurin yawan cin kwallaye a gasar zakarun Turai.

Sai dai Messi na gaban Ronaldo wurin yawan lashe wasu kofuna da kuma zira kwallo a gasar La Liga.

Real ta ci kwallon farko ta hannun Cristiano Ronaldo minti 10 da fara wasa, yayin da minti 19 tsakani Girona ta farke ta hannun Cristhian Stuani.

Bayan da aka dawo daga hutu ne Cristiano Ronaldo ya kara na biyu, sannan Lucas Vazquez ya kara na uku, sai Cristiano Ronaldo y ci na hudu kuma na uku da ya ci a karawar.

Cristhian Stuani ne ya kara farkewa Girona kwallo na biyu, inda Real ta kara na biyar ta hannun Gareth Bale.

Girona ta ci kwallo na uku ta hannun Juanpe, sai dai kuma Real Madrid ta ci na shida ta hannun Cristiano Ronaldo kuma na hudu a wasan.

Da wannan sakamakon Real Madrid ta koma ta uku a kan teburi da maki 60.

Cristiano Ronaldo ya ci kwallo 37 a kakar bana a Real Madrid, ciki har da 21 da ya zura a wasa 11 na baya-bayan nan.

Kwallo 21 a wasa 11 - gagarumar bajintar Ronaldo

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Cristiano Ronaldo ya lashe kyautar Ballon d'Or - ta gwarzon dan kwallon duniya - sau biyar

Lahadi, 21 Janairu, La Liga - Real Madrid 7-1 Deportivo La Coruna (Ronaldo 2)

Asabar, 27 Janairu, La Liga - Valencia 1-4 Real Madrid (Ronaldo 2)

Asabar, 3 Fabrairu, La Liga - Levante 2-2 Real Madrid (Ronaldo bai ci kwallo ba)

Asabar, 10 Fabrairu, La Liga - Real Madrid 5-2 Real Sociedad (Ronaldo 3)

Laraba, 14 Fabrairu, Zakarun Turai - Real Madrid 3-1 Paris St-Germain (Ronaldo 2)

Lahadi, 18 Fabrairu, La Liga - Real Betis 3-5 Real Madrid (Ronaldo 1)

Asabar, 24 Fabrairu, La Liga - Real Madrid 4-0 Alaves (Ronaldo 2)

Asabar, 3 Maris, La Liga - Real Madrid 3-1 Getafe (Ronaldo 2)

Talata, 6 Maris, Zakarun Turai - Paris St-Germain 1-2 Real Madrid (Ronaldo 1)

Asabar, 10 Maris, La Liga - Eibar 1-2 Real Madrid (Ronaldo 2)

Lahadi, 18 Maris, La Liga - Real Madrid 6-3 Girona (Ronaldo 4)

Labarai masu alaka