Wutar Daji ta kona gidaje a Ostreliya

Wutar ta yi barna mai yawa a jihar Victoria mai makwaftaka da jihar New South Wales Hakkin mallakar hoto SIMON WARD
Image caption Wutar ta yi barna mai yawa a jihar Victoria mai makwaftaka da jihar New South Wales

Masu kashe gobara a jihar New South Wales da ke kasar Ostreliya, sun ce sama da gidaje saba'in ne su ka kone a wata wutar daji da ta tilastawa daruruwan jama'ar jihar tserewa.

Masu bayar da agajin gaggawa sun bayyana cewa wutar ta fara lafawa, amma za'a dauki tsawon kwanaki kafin a kashe ta gaba daya. Gidaje da dama da wata makaranta a garin Tathra sun kone, inda jama'ar garin su ka tsere domin kubucewa wutar.

Rahotanni sun nuna cewa wutar ta mamaye Tathra yayin da yanayin zafi ya kai maki 38 a ma'aunin yanayi na Celcius. Kuma iska mai karfi ta rika rura wutar. Masu kashe gobara dari da hamsin ne su ka raba dare wajen kokarin kashe wutar wacce a yanzu ta lafa.

A na dai zaton tsawa ce ta yi sanadiyyar wutar dajin. Wutar ta yi barna mai yawa a jihar Victoria mai makwaftaka da jihar New South Wales.

Labarai masu alaka