'Pogba ba zai ji dadin halin da yake ciki ba'

United Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption United za ta buga wasan daf da karshe da Tottenham a kofin FA a Wembley

Kocin tawagar kwallon kafar Faransa, Didier Deschamps ya ce Paul Pogba ba zai yi farinciki da rashin buga wa Manchester United wasanni akai-a kai ba.

Pogba yana cikin tawagar kwallon kafar Faransa da za su buga wasan sada zumunta da Colombia da Rasha, duk da United ba ta sa shi a karawar da ta ci Brighton a kofin FA ba.

Deschamps ya ce ''Yana da tabbacin cewar Pogba ba zai so ya dunga zama a benci ko kuma kin saka shi a wasa ba''.

United za ta buga wasan Gasar Cin Kofin Premier da Swansea City a ranar 31 ga watan Maris.

Pogba ya buga karawar da Sevilla ta ci United a Gasar Cin Kofin Zakarun Turai, bayan da bai yi wasan Premier da Liverpool ba, sakamakon jinya da ya yi.

Pogba ya sake komawa United a shekarar 2016 kan kudi fam miliyan 89, inda ya taimaka wa kungiyar ta ci League Cup da Europa a kakar da ta gabata.

Labarai masu alaka