United ta tsawaita zaman Yound a Old Traffiord

United Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Young yana cikin 'yan wasan da Ingila ta bai wa goron gayyata a wasan sada zumunta da za ta yi

Kungiyar Manchester United ta tsawaita zaman Ashley Young zuwa shekara daya, domin ya ci gaba da murza-leda a Old Trafford.

Dan wasan mai shekara 32, ya koma United daga Aston Villa a shekarar 2011 a matakin dan wasan gaba na gefe, amma yanzu ya koma mai tsaron baya a kungiyar.

Young ya lashe Kofin Premier da na FA da League Cup da na Europa a zaman da yake yi a Old Trafford.

Dan kwallon ya buga karawa 29 a kakar shekarar nan, inda ya ci kwallo biyu, ya kuma koma buga wa tawagar kwallon kafa ta Ingila tamaula.