'Yan Madrid 20 aka gayyata tawagar kasashensu

Real Madrid Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption A karshen mako za a buga wasannin sada zumunta

Kimanin 'yan wasan Real Madrid 20 ne aka gayyata tawagar kwallon kafar kasashensu, domin buga musu tamaula a karshen mako.

'Yan wasan da za su buga wa kasashensu wasan sada zumunta a karshen mako sun hada da Sergio Ramos da Nacho da Isco da Asensio da Lucas Vazquez da Carvajal da Varane.

Sauran sun hada da Bale da Kroos da Casemiro da Marcelo da Modric da Kovacic da Keylor Navas da Cristiano Ronaldo da kuma Achraf.

Su kuwa Vallejo da Ceballos da kuma Mayoral za su buga wa Spaniya wasan neman shiga gasar cin kofin Turai da za a yi a shekarar 2019.

Shi kuwa Lucas zai halarci karawar da Spaniya za ta yi gida da waje da Amurka a wasan neman gurbin shiga gasar matasa 'yan kasa da shekara 20 da za a yi a Faransa.

Labarai masu alaka