Ko Pogba da Neymar za su buga kwallo a kungiya daya?

Neymar Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Pogba zai buga wa Faransa wasan sada zumunta a karshen mako

Dan wasan Manchester United, Paul Pogba ya ce yana fatan wata rana zai murza-leda kungiya daya da Neymar.

Neymar ya yabi kwazon Pogba a shekara biyu da suka wuce, inda ya ce salon wasan dan kwallon tawagar Faransa zai da ce da taka-leda a Barcelona.

Sai dai kuma yana yi ya sauya inda ba za su iya wasa tare a Nou Camp ba, bayan da Neymar ya koma Paris St-Germain a kakar shekarar nan.

Shi kuwa Pogba ya bar Juventus a watan Agustan 2016, inda ya sake komawa Manchester United da taka-leda.

Pogba na fatan wata rana zai buga tamaula da Neymar, ya kuma ce yana tuna abinda dan kwallon Brazil din ya fada a kanshi, zai so ya yi wasa tare da shi.

Ya kuma kara da cewar ''A Brazil kwallon kafa ita ce rayuwa, kowa yana buga tamaula, ina jin dadin kallon yadda yake murza-leda, yana da dabaru, ya lakanci kwallon kafa, sannan ya iya buga wasa, ina jin dadin kallon yadda yake buga kwallo''.