Messi na atisaye a Manchester City

Lionel Messi Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Argentina za ta buga gasar cin kofin duniya a Rasha

Lionel Messi na yin atisaye a filin wasa na Manchester City tare da tawagar kwallon kafar Argentina.

Argentina ta zabi filin City domin yin atisayen tunkarar wasan sada zumunta da za ta yi da Italiya a Etihad a ranar Juma'a.

A ranar Talata Messi ya isa filin wasa na City, inda ya motsa jiki tare da sauran tawagar Argentina daga karshe aka bai wa 'yan jarida damar yin magana da 'yan wasa.

Sauran 'yan kwallon Argentina da suke filin Manchester City har da Sergio Aguero wanda ke yin jinya da Nicolas Otamendi.

Haka kuma Gonzalo Higuain da Angel Di Maria da Javier Mascherano da kuma Marcos Rojo duk sun halarci motsa jikin.

Labarai masu alaka