​​Fitattun 'yan wasa 5 da ya kamata ku sansu​

Jadon Sancho Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Dan kasar Ingila ne amma yana murza-leda a Jamus ya kamata ku san shi

Shin kun gaji da jin labarin Messi ko Ronaldo da kuma Neymar?

BBC na gabatar muku da 'yan wasa biyar da baku sansu ba, wadanda za su iya kafa tarihi a fagen tamaula a duniya.

1. Pietro Pellegri (Mai shekara 17, Italiy da Monaco)

Ana kiransa da sunan "sabon Messi", yana da shekara 15 ya fara kafa tarihi a Genoa a Gasar Serie A: Matashin da ya fara buga gasar kuma ya ci kwallo biyu rigis a wasa.

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Pietro Pellegri ya cika shekara 17, kuma yana koyon darasin tamaula

Wasu manyan kungiyoyin kwallon kafar Turai sun yi kokarin sayen dan wasa, amma ya zabi Monaco wadda ta saye shi kan $24m a watan Janairu, a matsayin na biyu matashin da aka saya mafi tsada.

Har yanzu bai shiga cikin babbar kungiyar ba, amma tun da ya kai shekara 17 yana saka kaimi a wasannin da yake yi.

2. Justin Kluivert (Shekara 18, Netherlands da Ajax)

Idan ka ji sunan babu wanda za ka tuna illa mahaifinsa Kluivert - Justin dan gidan Patrick ne, tsohon dan wasan Holland da Barcelona wanda ya taka-leda a Newcastle.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Justin Kluivert zai buga wa Holland a karon farko wasan sada zumunta da za ta yi da Ingila da Portugal.

Kamar yadda mahaifinsa ya yi, Justin na cin kwallayen da ya haskaka shi a koda yaushe a jax. Ya kuma taba cin kwallo uku a wasa, abinda mahaifinsa bai yi a gasar Netherlands.

Manchester United da Barcelona na rige-rigen daukar dan wasa kuma tuni tawagar kwallon kafar Holland ta gayyace shi wasan sada zumunta da za ta yi da Ingila da kuma Portugal.

3. Jadon Sancho (Shekara 17, Ingila, Borussia Dortmund)

Wanda ake kira da sunan "Neymar Ingila", Sancho ya yi atisaye a Watford da kuma Manchester City har zuwa bara - daga baya ya koma Borussia Dortmund kan dala miliyan 14.

Dan wasan bai amince ya zauna karkashin Pep Guardiola a Manchester City, inda ya koma Jamus domin ya dunga buga wasanni akai-akai.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Jaridun Ingila sun ce duk da ba a gayyaci Jadon Sancho wasan sada zumunta ba, amma zai iya buga gasar Kofin duniya a Rasha a 2018

Yana cikin matasan Ingila da suka lashe kofin duniya na masu shekara 17, sai dai yarjejeniyar da aka yi da kungiyarsa shi ne ya buga wa tawagar kwallon kafar Ingila wasannin cikin rukuni.

Jaridun Ingila sun yi tsokaci kan rashin gayyatar sa wasannin sada zumunta da za ta buga a karshen mako, amma sun ce yana da kyau a kai shi gasar cin kofin duniya da za a yi a Rasha.

4. Vinicius Júnior (Shekara 17, Brazil, Real Madrid yana wasa aro a Flamengo)

Kasa da minti 20 ya yi yana taka-leda Real Madrid ta tabbatar da cewar zai zama fitatcen dan kwallo a nan gaba, inda ta dauki dan wasan Brazil kan dala miliyan 54.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Vinicius Junior zai koma buga gasar Turai nan gaba

Saboda haka sai ya shekara 18 zai iya komawa Spaniya, saboda haka ya ci gaba da zama a kungiyarsa ta Flamengo.

A bara ya jagoranci tawagar kwallon kafar Brazil ta lashe kofin kudancin Amuka na matasa 'yan shekara 17. kuma shi ne ya zama kan gaba a cin kwallaye a gasar kuma wanda ya fi yin fice a wasannin.

Idan ya cika shekara 18 a watan Yuni zai koma Real Madrid inda zai samu kwarewar da yake bukata.

5. Jan-Fiete Arp (Shekara 18, Hamburg, Jamus)

A bara yana da shekara 17, Arp ya zama na farko da aka haifa a shekarar 2000 ya fara buga gasar Bundesliga ya kuma ci kwallo.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Dan kasar Ingila ne amma yana murza-leda a Jamus ya kamata ku san shi

Hukumar kwallon kafar Turai ta ce, "Daya ne daga matasan da za su haskaka a gasar kwallon Jamus''.

Dan wasan ya ci kwallo bakwai a gasar matasa 'yan shekara 17 ta nahiyar Turaihe a bara, haka kuma ya zura kwallo biyar a gasar cin kofin duniya. dan kwallon yaki yadda ya koma Chelsea da murza-leda, amma yanzu ana cewa Bayern Munich ce ke zawarcin sa.

Labarai masu alaka

Karin bayani