'Yan wasan da ke kan gaba a cin kwallo a Turai

Top Scorers Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Salah ne kan gaba da kwallo 28 a gasar Premier Ingila

Hukumar kwallon kafa ta duniya ta ware wannan makon a matsayin ranakun da kasashe za su buga wasannin sada zumunci a tsakanin su.

Hakan ne ya sa ake yin hutu a manyan gasar kasashen Turai, inda wasu 'yan wasa ke kan gaba a cin kwallaye.

Mohammed Salah ne ke kan gaba a Premier da kwallo 28, bayan da aka yi wasa 31 a gasar, kuma shi ne na daya a Turai.

A spaniya kuwa, bayan da aka yi wasannin mako na 29, Lionel Messi na Barcelona ne da kwallo 25 ke kan gaba.

A kasar Italiya an kammala wasannin mako na 29 a gasar Serei A, inda Ciro Immobile na Lazio ne kan gaba da kwallo 24.

A jamus kuwa Robert Lewandowski ne na daya dan wasan Bayern Munich, bayan da ya ci 23, bayan da aka buga karawar mako na 27.

An buga wasannin mako na 31 a gasar cin kofin kasar Faransa, inda Edison Cavani ne ke kan gaba da kwallo 24 a raga.

Labarai masu alaka