Damben Bahagon Musa da Dogon Washa
Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Damben Bahagon Musa da Dogon Washa

Sama dambe Bakwai aka yi a gidan wasa na Ali Zuma da ke unguwar Dei-Dei a Abuja, Nigeria a safiyar Lahadi.

Mohammed Abdu ne ya hada rahoton

Sai dai kuma dukkan wasannin da aka yi canjaras aka tashi, babu wanda ya dafa kasa a dambatawar da aka yi.

Sakamakon wasanni takwas da aka yi babu kisa:

  • Garkuwan Ebola daga Kudu da Shagon Dan Aguro daga Arewa
  • Shagon Buzu daga Arewa da Shagon Autan Na Dutsen Mari Guramada
  • Autan Faya daga Kudu da Shagon Sojan Kyallu Guramada
  • Dogon Washa Guramada da Shagon Bahagon Musan Kaduna daga Arewa
  • Bahagon Dan Kanawa daga Kudu da Shagon Bahagon Ayo daga Arewa
  • Shagon Shagon Alhazai daga Arewa da Bahagon Dan Sama'ila daga Kudu
  • Bahagon Sisco daga Kudu da Bahagon Shamsu Kanin Emi daga Arewa