Ronaldo na kara kafa tarihin cin kwallaye

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Portugal ta doke Masar 2-1 a wasan sada zumunta a ranar Juma'a

Dan wasan tawagar kwallon kafar Portugal da Real Madrid, Cristiano Ronaldo na kara kafa tarihin cin kwallo a Portugal.

Dan wasan shi ne ya ci Masar kwallo biyu a wasan sada zumunta da suka yi nasara da ci 2-1 a ranar Juma'a.

Da wannan sakamakon Ronaldo ya ci wa tawagar kwallon kafa ta Portugal kwallo 81 jumulla, kuma shi ne na uku a kasar a yawan zura kwallo a raga.

Tun bayan da Portugal ta yi wasa 21, bayan da ta lashe kofin nahiyar Turai, Ronaldo ya buga karawa 15 daga ciki, inda ya ci kwallo 20, sannan ya taimaka aka ci hudu a raga.

Wasa biyu da Portugal ta buga da babu hannun Ronaldo a cin kwallo, shi ne wanda ta yi da Chile a Confederation Cup da na Switzerland a wasan neman gurbin zuwa gasar kofin duniya.