'Yan Madrid da Zidane ya fi amfani da su a wasa

Real Madrid Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Real za ta kara da Juventus a wasan daf da na kusa da na karshe a Zakarun Turai

Real Madrid ta nada Zinadine Zidane a matsayin kocinta, bayan da ta sallami Rafael Benitez a ranar a 4 ga watan Janairun 2016.

Zidane din ya jagoranci Madrid wasa 135, inda ya ci 97, sannan ya yi canjaras a wasa 24 aka doke shi sau 14, haka kuma ya ci kwallo 361, bayan da aka ci Real kwallo 142.

Haka kuma tun lokacin da aka bai wa Zidane ragamar Madrid, ya saka Lucas Vazquez da Cristiano Ronaldo da Isco da Marcelo da Kroos da kuma Benzema a wasa sama da 100.

Lucas Vazquez wanda ya buga wasa 41 a kakar bana, shi ke kan gaba, inda ya buga fafatawa 109 karkashin kocin Zidane.

Cristiano Ronaldo ya buga wasa 105 kuma shi ne na biyu a jeren wadanda suka buga wasanni da dama karkashin kocin.

Dan wasa Marcelo da kuma Kroos sun yi wasa 103 kowannen su, shi kuwa Benzema fafatawa 101 ya yi.

Real Madrid tana ta uku a kan teburin gasar La Liga da maki 60, za kuma ta ziyarci Las Palmers a wasan gaba da za ta buga a La Liga.

Labarai masu alaka