UEFA ta yi sabbin gyare-gyare a dokokinta

UEFA Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Coutinho ya koma Barcelona, amma baya buga Gasar Zakarun Turai

Hukumar kwallon kafar nahiyar Turai ta yi garare-gyare a Gasar Zakarun Turai, wadda take gudanarwa, domin bunkasa wasannin.

Daga cikin gyare-gyaren, a yanzu an yarda dan kwallo ya buga wa sabuwar kungiyar da ta saye shi wasannin Gasar Champions League da ta Kofin Europa ko da a kakar ya buga wa tsohuwar kungiyarsa.

Sai dai dokar za ta fara aiki ne a kakar badi, lokacin an kammala gasar Champions League da ta Europa na bana.

Haka kuma hukumar ta amince a yi sauyin dan kwallo a karo na hudu a maimakon uku da ake yi yanzu, amma a wasannin zagaye na biyu a gasar, kuma sai an kai ga karin lokaci, idan kungiyoyin sun kammala minti 90 babu ci.

Saboda haka kungiyoyi za su rika bayyana 'yan wasa 23 a Champions League da Kofin Europa a maimakon 18, domin samun damar zabar dan kwallo na hudu da zai shiga karawar.

UEFA ta kuma ce za ta dinga gabatar da wadansu wasannin cikin rukuni da wuri wato da karfe 5.55 agogon GMT.