Barcelona za ta dauki Luke Shaw

Manchester United Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Mourinho yana ta sukar Shaw kan yadda yake buga kwallo a United

Kungiyar Barcelona na duba idan za ta iya sayen dan kwallon Manchester United, mai tsaron baya Luke Shaw.

Dan wasan mai shekara 22, na shan suka a wajen Jose Mourinho kan rawar da yake takawa a wasannin da yake yi in ji Mirror.

Jaridar Mail kuwa ta wallafa cewar Monaco ta shiga jerin kungiyoyin da ke son sayen Maroune Fellaini daga Manchester United.

Yarjejeniyar da dan kwallon mai shekara 30 ya saka hannu da United, za ta kare a karshen kakar bana, kuma ana sa ran zai bar Old Trafford idan ta cika.

Mai tsaron ragar Liverpool, Simon Mignolet ya ce zai yi kokari ya karbi gurbin buga wa kungiyar wasanni akai-akai in ji The Sun.

Mai tsaron ragar mai shekara 30, ya ce ba zai bar kungiyar ba, zai ci gaba da murza-leda a Anfield.

Kocin Arsenal, Arsene Wenger ya ce yana son Jack Wilshere ya ci gaba da zama a kungiyar.

Wilshere dan wasan tawagar Ingila, bai amince da tayin da aka yi masa na rage masa albashi ba, idan har yana son zama a Gunners in ji Star.

Labarai masu alaka