Serbia ta lallasa Super Eagles da ci 2-0

Super Eagles Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Super Eagles za ta buga Gasar Cin Kofin duniya da za a yi a Rasha

Tawagar kwallon kafa ta Nigeria ta yi rashin nasara a hannun Serbia da ci 2-0 a wasan sada zumunta da suka buga a ranar Talata a Landan.

Serbia ta ci kwallayen ta hannun Aleksandar Mitrovic, inda ya ci ta farko bayan da aka dawo daga hutu, sannan ya kara na biyu saura minti 10 a tashi daga karawar.

Nigeria ta yi nasarar cin Poland a ranar Juma'a a wasannin da take yi domin tunkarar gasar cin kofin duniya da za a yi a Rasha a bana.

Nigeria tana rukuni daya da ya hada da Croatia da Iceland da kuma Argentina.