Spaniya ta shararawa Argentina kwallaye

Spain Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Wannan ne karon farko da Spaniya ta ci tawagar da ke da kofin duniya kwallaye da yawa

Tawagar kwallon kafa ta Spaniya ta doke ta Argentina da ci 6-1 a wasan sada zumunta da suka kara a ranar Talata.

Spaniya ta ci kwallayen ne ta hannun Diego Costa da Thiago Alcantara da Iago Aspas da kuma Isco wanda ya ci uku rigis a karawar.

Ita kuwa Argentina wadda Messi bai buga mata fafatawar ba, ta ci kwallo ne ta hannun Otamendi tun kafin a tafi hutu.

Spaniya tana rukuni na biyu a gasar cin kofin duniya da ya kunshi Iran da Morocco da kuma Portugal.

Argentina kuwa tana rukuni na hudu da ya hada da Iceland da Croatia da kuma Nigeria.

Labarai masu alaka