Na so Man Utd ta yi irin salon wasan Man City – Van Gaal

Van Gaal
Bayanan hoto,

United ta sallami Van Gaal ne a shekarar 2016

Tsohon Kocin Manchester United Louis van Gaal ya ce ya so kungiyar ta yi irin salon wasan da Manchester City take yi yanzu karkashin jagorancin Pep Guardiola.

Dan asalin kasar Netherlands din ya sha suka lokacin da yake jan ragamar United saboda salon da yake amfani da shi, musamman lokacin da kungiyar ta samu nasara a wasanni hudu kacal cikin 16 da ta buga.

Sai dai an sallame shi ne a shekarar 2016, inda Jose Mourinho ya maye gurbinsa.

Ya ce 'yan wasan Guardiola suna bukatar su samu nasara ne a wasanni biyu kawai gabanin su lashe gasar Firimiyar bana, saboda sun hada jumullar maki 81 yanzu daga wasanni 30 da suka buga.

"Pep Guardiola mutumi na ne, don a halin yanzu shi ne kocin da ya fi kowa a gasar Firimiya. Guardiola ya mayar da City wani inji, " in ji Van Gaal.

"Yana irin salon wasan da na so yi a lokacin da nake United. Amma shi ya yi sa'ar samun kwararrun 'yan wasa. Amma da ni ne da abin ya dauki dogon lokaci. Kodayake ban samu lokacin ba," in ji shi.

Sai dai ya musanta zargin cewa ba sa jituwa da mutumin da ya maye gurbinsa a United.

Amma ya soki daya daga cikin manyan shugabannin kungiyar Ed Woodward wanda ya ce ya saba alkawarin da ya daukar masa bayan lashe kofin FA.

Karanta wadansu karin labarai