Jack Wilshere: Ko a kwai takaddama tsakanin Arsenal da Ingila

Jack Wilshere Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Rabon da Jack Wilshere ya buga wa Ingila wasa tun gasar cin kofin Euro 2016

Arsenal ta ce 'babu wata takaddama' tsakaninta da Ingila bayan da Jack Wilshere ya samu rauni a lokacin da ya ke atisaye da tawagar kasar.

Wilshere, mai shekara 26, ka iya taka-leda a wasan Arsenal da Stoke ranar Lahadi duk da cewa bai buga wasannin sada zumuntar da Ingila ta yi da Netherlands da kuma Italiya ba.

Mataimakin manajan Arsenal Steve Bould, wanda ya yi magana a madadin Arsene Wenger, ya ce dawowar Wilshere rigakafi ne kawai saboda rashin lafiyar da ya yi fama da ita.

"Jack ya dan samu rauni a gwuiwarsa, ya dawo gida kuma ya samu sauki," a cewar Bould.

"A iya sani na babu wata matsala [da Ingila]."

Bould ya kara da cewa dan wasan gaba na Faransa Alexandre Lacazette zai iya dawowa cikin tawagar a karawar da za su yi da Stoke bayan raunin da ya yi fama da shi.

Arsenal tana mataki na shida a teburin Firimiya, maki 13 a bayan Tottenham wacce ke mataki na hudu yayin da ya rage wasa takwas a kammala kakar bana.

Labarai masu alaka

Labaran BBC

Shafuka masu alaka

BBC ba tada alhaki game da shafukan da ba nata ba