Dan wasan Man Utd na son buga wa Najeriya kwallo

Tosin Kehinde Hakkin mallakar hoto Getty Images

Dan wasan karamar kungiyar Manchester United Tosin Kehinde ya ce a shirye yake ya taka wa tawagar Najeriya leda.

Kehinde mai shekara 19, wanda yake wasa a karamar kungiyar United 'yan kasa da shekara 23 yana da damar buga wa Najeriya, ko kuma Ingila wasa, amma ya ce shi ya fi son Najeriya.

"A kodayaushe ina tare da Najeriya. An haife ni a can. Duka 'yan gidanmu 'yan Najeriya. Na fito daga gidan da suke da iko sosai akaina," in ji dan kwallon.

A ranar Lahadin da ta gabata ne dan wasan ya gana da shugabannin hukumar kwallon kafa ta Najeriya (NFF) don fara bin matakan da za su ba shi damar yi wa Super Eagles wasa.

Dan kwallon ya gana ne da jami'an tare da rakiyar iyayensa a birnin Landan.

Kehinde ya ce yana so ne ya zama kamar dan wasan Arsenal Alex Iwobi wanda shi ma, a shekarar 2015, ya zabi yi wa Najeriya wasa a maimakon kasar Ingila.

An haifi dan wasan ne a birnin Legas amma ya tashi ne a Birtaniya.

Ya kuma koma karamar kungiyar United ne lokacin da yake da shekara 13, kodayake ya ce a yanzu yana da burin yi wa babbar kungiyar United wasa.

Karanta wadansu karin labarai

Labarai masu alaka