Sau nawa Juventus ta taba doke Madrid?

Madrid ta doke Juventus da ci 4-1 a wasan karshe na gasar zakarun Turai na bara Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Madrid ce ta doke Juventus da ci 4-1 a wasan karshe na gasar zakarun Turai na bara

A ranar Talata ne Juventus za ta karbi bakuncin Real Madrid a wasan gab da na kusa da na karshe a gasar Zakarun Turai.

A bara dai Madrid ce ta doke kungiyar a wasan karshe na gasar, abin da ya ba ta damar daukar kofin gasar a birnin Cardiff na kasar Birtaniya.

A koawace karawa da Madrid ta taba yi da Juventus, Ronaldo yana samun zura kwallo a raga.

Sau 19 kungiyoyin suna haduwa a tarihin gasar Zakarun Turai -Madrid ta yi nasara a wasanni tara, yayin da Juventus ta samu nasara a wasanni takwas, sun kuma yi kunnen doki a wasanni biyu.

Hakazalika, duka kungiyoyin biyu kowace ta zura wa abokiyar karawarta kwallaye 22 ne a raga a tarihin karawarsu.

Tawagar Real Madrid

Masu tsaron gida: Keylor Navas, Casilla da Luca

'Yan wasan baya: Carvajal, Vallejo, Ramos, Varane, Nacho, Marcelo, Theo da Achraf.

'Yan wasan tsakiya: Kroos, Modric, Casemiro, Llorente, Asensio, Isco, Kovacic da Ceballos.

'Yan wasan gaba: Cristiano Ronaldo, Benzema, Bale, Lucas Vázquez da kuma Mayoral.

Tawagar Juventus

Hakkin mallakar hoto MARCO BERTORELLO
Image caption Juventus za ta yi kokarin ganin ta rama cin Madrid ta yi mata bara

Masu tsaron gida: Buffon, Szczesny da De Sciglio

'Yan wasan baya: Barzagli, Marchisio, Chiellini, Asamoah, Rugani, Lichtsteiner da Alex Sandro

'Yan wasan tsakiya: Khedira, Bentancur, Matuidi, Pinsoglio, Cuadrado, Bentancur, Sturaro da Marchisio

'Yan wasan gaba: Higuaín, Douglas Costa, Mandžukić da Dybala.

Labarai masu alaka