'Yan wasan Madrid da suka kara da Juventus

Asalin hoton, Getty Images
Madrid ce ta doke Juventus da ci 4-1 a wasan karshe na gasar Zakarun Turai na bara
A ranar Talata ne Juventus ta karbi bakuncin Real Madrid a wasan gab da na kusa da na karshe a gasar Zakarun Turai.
Real ta samu nasara da ci 3-0 inda Ronaldo ya ci biyu sannan Marcelo ya ci daya.
A bara dai Madrid ce ta doke kungiyar a wasan karshe na gasar, abin da ya ba ta damar daukar kofin gasar a birnin Cardiff na kasar Birtaniya.
A koawace karawa da Madrid ta taba yi da Juventus, Ronaldo yana samun zura kwallo a raga.
Ko wadanne 'yan wasa ne za su taka-leda a kungiyoyin biyu?
Tawagar Real Madrid
Masu tsaron gida: Keylor Navas, Casilla da Luca
'Yan wasan baya: Carvajal, Vallejo, Ramos, Varane, Nacho, Marcelo, Theo da Achraf.
'Yan wasan tsakiya: Kroos, Modric, Casemiro, Llorente, Asensio, Isco, Kovacic da Ceballos.
'Yan wasan gaba: Cristiano Ronaldo, Benzema, Bale, Lucas Vázquez da kuma Mayoral.
Tawagar Juventus
Asalin hoton, MARCO BERTORELLO
Juventus za ta yi kokarin ganin ta rama cin Madrid ta yi mata bara
Masu tsaron gida: Buffon, Szczesny da De Sciglio
'Yan wasan baya: Barzagli, Marchisio, Chiellini, Asamoah, Rugani, Lichtsteiner da Alex Sandro
'Yan wasan tsakiya: Khedira, Bentancur, Matuidi, Pinsoglio, Cuadrado, Bentancur, Sturaro da Marchisio
'Yan wasan gaba: Higuaín, Douglas Costa, Mandžukić da Dybala.
Sau 19 kungiyoyin suna haduwa a tarihin gasar Zakarun Turai - Madrid ta yi nasara a wasanni tara, yayin da Juventus ta samu nasara a wasanni takwas, sun kuma yi kunnen doki a wasanni biyu.
Hakazalika, duka kungiyoyin biyu kowace ta zura wa abokiyar karawarta kwallaye 22 ne a raga a tarihin karawarsu.