Aguero ba zai buga wasan City da Liverpool ba

Asalin hoton, PA
Sergio Aguero ya halarci atisayen Argentina a makon da ya wuce amma bai take-leda ba
Dan wasan gaba na Manchester City Sergio Aguero ba zai buga wasan da kungiyar za ta kara da Liverpool ranar Laraba saboda raunin da yake fama da shi a gwuiwarsa.
Kungiyoyin biyu za su kara ne a wasan gab da na kusa da na karshe na gasar cin kofin Zakarun Turai a gidan Liverpool.
Aguero bai buga wasa biyar na baya da City ta yi ba da kuma na kasarsa ta Argentina saboda raunin.
"Yanayin Sergio ya inganta sosai amma likitoci sun sun yi magana da shi yau inda suka ce har yanzu da dan sauransa," a cewar kociya Pep Guardiola.
Liverpool ma na da matsala a bayanta saboda duka Joe Gomez da Joel Matip da Ragnar Klavan ba za su taka-leda a wasan ba saboda rauni.