'Yan Barca 18 da suka ragargaza AS Roma

Barcelona da Roma

Asalin hoton, Barcelona.com

Bayanan hoto,

Barcelona ta doke Roma da ci 6-1 a karawar karshe da suka yi

A ranara Laraba ne Barcelona ta karbi bakuncin AS Roma a wasan dab da na kusa da na karshe a gasar cin kofin Zakarun Turai.

Barca ta yoi nasara da ci 4-1

Da ma ana ganin Barcelona, wacce ke kan gaba a teburin La Liga kuma har yanzu ba a doke ta a wasa fiye da 30, ita ce za ta kai bantanta a wasan.

Amma wasu masu sharhi na ganin ba a san maci tuwo ba sai miya ta kare - domin Roma ma ba kanwar lasa ba ce.

Za mu kawo muku sharhi kai tsaye kan wannan wasa da ma karawa tsakanin Liverpool da Manchester City a BBCHAUSA.COM da misalin karfe 06.30 na yamma.

ga jerin 'yan wasan da suka wakilci kungiyoyin biyu:

Ter Stegen, Cillessen, Semedo, Piqué, Rakitic, Sergio, Denis Suárez, Iniesta, Suárez, Messi, Dembélé, Paulinho, Alcácer, Jordi Alba, Sergi Roberto, André Gomes, Umtiti da Vermaelen.

Itama AS Roma za a iya cewa ta kimtsa tsaf domin tunkarar wannan wasa sai dai za ta fita ne ba tare da 'yan wasanta Radja da Pellegrini ba saboda raunin da suke fama da shi.

Ga jeroin 'yan wasan da za su fafata:

Alisson Becker, Andrea Romagnoli, Lukasz Skorupski, Juan Jesus, Aleksandar Kolarov, Elio Capradossi, Federico Fazio, Alessandro Florenzi, Bruno Peres, Kostas Manolas, Radja Nainggolan, Kevin Strootman, Lorenzo Pellegrini, Daniele De Rossi, Maxime Gonalons, Gerson, Diego Perotti, Edin Dzeko, Patrik Schick, Gregorie Defrel da Stephan El Shaarawy.

Asalin hoton, ASroma.com

Bayanan hoto,

'Yan wasan AS Roma sun ce sun shirya tsaf domin tunkarar Barcelona