Kwallon Ronaldo ta girgiza duniyar tamaula

Asalin hoton, Getty Images
Cristiano Ronaldo ya yi tsalle sama kafin ya ci kwallon duk da cewa ba ya kallon ragar
Kwallon da dan wasan Real Madrid Cristiano Ronaldo ya ci Juventus a wasan da madrid ta yi nasara da ci 3-0 na ci gaba da jan hankalin ma'abota kwallon kafa a duniya.
Ronaldo, mai shekara 33, ya yi tsalle sannan ya daki kwallon da baya (acrobatic) a minti na 64 da fara wasan.
Ita ce kwallo ta biyu da ci a ranar, bayan da ya fara bude ragar Juventus a minti na uku da fara karawar.
Duka magoya bayan Juventus da na Madrid sun rinka tafa wa dan wasan, abin da ya nuna cewa kwallon ta kai makura wurin kyau.
Wannan ya sa wasu ke cewa ita ce kwallo mafi kyau da aka ci a tarihin gasar Zakarun Turai, ko ma kwallon kafa baki daya.
Wasu kuma suka ce ita ce mafi kyau da Ronaldo ya taba ci a rayuwarsa ta kwallon kafa.
Mai yi wa BBC sharhi kan al'amuran wasanni Pat Nevin, ya ce "tana cikin kwallo mafi kyau da aka taba ci a tarihin murza-leda a duk duniya".
Ronaldo da kansa

Asalin hoton, Getty Images
Sau biyu Ronaldo na zura kwallo a ragar Gianluigi Buffon a wasan
Jama'a na magana a kan kwallo ta biyu, kwallo ce mai ban sha'awa, mai yiwuwa mafi kyau da na taba zurawa", a cewar Ronaldo bayan kammala wasan.
Daya daga cikin kwallo mafi kyua a tarihi
Golan Juventus Gianluigi Buffon: "Ronaldo dan wasa ne da ya kai makura... Za a iya kwatanta shi da Diego Maradona da kuma Pele."
Dan wasan baya na Juventus Andrea Barzagli: "Cristiano shi ya shirya kwallo ta biyu. Kai ka ce wasan kwaikwayo ne na kwamfuta... Kwallo ce da za a dade ana maganarta a tarihi. Abin takaici ne a kanmu lamarin ya faru".
Kocin Real Madrid Zinedine Zidane: "Cristiano Ronaldo da ban ya ke a cikin saura. Kullum burinsa shi ne ya yi wata bajinta da babu wanda ya yi irinta a gasar Zakarun Turai. Kwallon da ya ci ta biyu abin al'ajabi ne, duk da cewa ya zubar da damarmaki biyu masu sauki. Haka kwallon kafa ta gada."
'Kwallon da na ci ta fi kyau'

Asalin hoton, AFP
Kwallon da Zinedine Zidane ya ci a filin wasa na Hampden Park da ke Glasgow
Amma wacce kwallo ce ta fi kyau - bari mu bar maganar ga Zinadine Zidane wanda shi ma ya ci wata kwallo mai ban mamaki a wasan karshe a gasar cin kofin Zakarun Turai da Real ta doke Bayer Leverkusen a 2002.
An tambaye shi ko wacce kwallo ce ta fi kyau, sai ya ka da baki ya ce...
Tawa mana! Hakika tawa ta fi.